Atiku Abubakar


Contributors to Wikimedia projects

Article Images

Atiku Abubakar (an haife shi ranar 25 ga watan Nuwamba shekarar 1946) ya kasance ɗan siyasan Najeriya kuma ɗan kasuwa ne wanda ya taba riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasar Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007 lokacin shugabancin Olusegun Obasanjo.[1][2][3] Atiku ya nemi zama gwamnan Jihar Adamawa a 1990, 1996 daga baya kuma, a 1998, aka zaɓe shi kafin nan ya zama mataimakin Olusegun Obasanjo a zaɓen 1999 na shugaban ƙasar Najeriya an kuma sake zaɓen su a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya ta 2003.[4]

Atiku Abubakar
mataimakin shugaban ƙasar Najeriya

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Mike Akhigbe - Goodluck Jonathan
Rayuwa
Haihuwa Jada (Nijeriya), 25 Nuwamba, 1946 (77 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Fulani
Harshen uwa Adamaua-Fulfulde (en) Fassara
Ƴan uwa
Abokiyar zama Amina Titi Atiku Abubakar
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a customs officer (en) Fassara da ɗan siyasa
Employers Najeriya
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress
atiku.org
Majar Atiku a jam'iyar APC

Farkon rayuwa

Atiku haifaffen jihar Adamawa ne.[5]

Siyasa

 
Atiku bayan zabe

Atiku Abubakar yayi rashin nasarar samun zama shugaban ƙasar Najeriya a matakai har sau biyar, na farko a 1993, 2007, 2011, 2015 da kuma 2019. A shekarar 1993, yayi takara a ƙarƙashin Social Democratic Party dan neman zama shugaban ƙasar amma ya sha kaye a wurin Moshood Abiola da Baba Gana Kingibe. Ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Action Congress a Zaɓen Shugaban ƙasar Najeriya ta 2007 amma yayi rashin nasara da zuwa na uku a wurin Umaru Yar'Adua na jam'iyyar PDP da Muhammadu Buhari na ANPP. Ya nemi zama ɗan takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam'iyyar People's Democratic Party lokacin Zaɓen Shugaban ƙasar Najeriya ta 2011 nan ma yayi rashin nasara a hannun shugaba mai ci Goodluck Jonathan.[6] A 2014, Atiku ya koma jam'iyyar APC gabanin Zaɓen Shugaban ƙasar Najeriya ta 2015 kuma ya nemi zama ɗan takarar jam'iyyar amma yayi rashin nasara a hannun Muhammadu Buhari. A shekarar 2017, ya sake komawa jam'iyyar PDP a inda kuma ya zama ɗan takarar jam'iyyar a Zaben Shugaban ƙasar Najeriya ta 2019, sai dai har wayau ya sake rashin nasara a hannun shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.[7][8]

Manazarta

  1. "Profile of Atiku Abubakar: From an only child of a father who opposed western education to a political guru". Nigeria Today. 2 October 2018. Retrieved 3 January 2019.
  2. Adeosun, Olajumoke (2019-07-17). "Atiku Abubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria". Entrepreneurs In Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-09. Retrieved 2020-05-29.
  3. "Atiku Abubakar - the Nigerian operator who knows how to make money". BBC News (in Turanci). 2019-02-06. Retrieved 2020-09-11.
  4. Podcast, N. L.; Giveaway, N. L. (2019-11-25). "Happy Birthday!! Atiku Abubakar Celebrates His 73rd Birthday (Drop Your Well Wishes) » Naijaloaded". Naijaloaded (in Turanci). Retrieved 2020-05-29.
  5. "The Story of My Life by Atiku Abubakar". PM News Nigeria. 15 April 2019.
  6. Adeosun, Olajumoke (2019-07-17). "Atiku Atiku AbAbubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria". Entrepreneurs In Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-09. Retrieved 2020-05-29.
  7. "Atiku emerges PDP presidential candidate". The Punch (in Turanci). 7 October 2018. Retrieved 2019-04-19.
  8. "2023: Where Nigeria's President comes from, not important ― Atiku". Vanguard News (in Turanci). 2021-10-07. Retrieved 2022-02-22.