Tarihin Hadejia Da Sarakunanta (6)


Idris Aliyu Daudawa

Article Images

8.Umaru bin Buhari,1863-1865

Bayan rasuwar Buhari a fagen daga ko yaki sai dansa Umaru ya zama Sarkin Hadejia na bakwai lokacin ya na da shekara 18.Ya samu damar hawan karagar mulkin ne ta taimakon Sarkin Arewa Tatagana da Sarkin yakin Hadejia Jaji, wanda shi ne mai fada aji kuma bawa na Buhari. (Taskar Suleiman Ginsau).Daular Usumaniyya ce ta amince da nada shi Sarkin a wani kokarin da ta ke  yi na maido da Hadejia karkashin daular Usumaniyya. Sai dai kuma Sarkin Hadejia Umaru ya yi sarauta ne ta shekara biyu, wani abu daban shekarun na da matukar muhimmanci.Kawunsa Haru yana sha’awar zama Sarkin Hadejia, saboda kuwa  a asirce yana kokarin yadda zai raba Umaru da ci gaba da kasancewa ko zama a matsayin Sarkin ta.Da farko sai da aka fara gamawa da Tatagana da  Jiji,wadanda sune suka fi kowa nuna goyon baya ga Umaru a wani shirin da ake yi na raba shi da sarautar.Da haka ne lokacin da Sarkin Hadejia   Umaru ya fita a tafiyar da ya kan yi ta zuwa Kogin Hadejia abin da ya faru shine sai wasu taga cikin ‘yan tawagar shi suka bar shi , suka kkuma hana shi komawa birnin Hadejia.Daga nan sai Sarkin Hadejia Umaru ya yi murabus zuwa Chamo karkashin masarautar Kano inda ya zauna har karshen rayuwarsa ya mutu a shekara 1920. (Taskar Suleiman Ginsau)

  1. Haru bin Sambo, 1865-1885

Da aka yi nasarar cire Umaru daga Sarautar Hadejia sai Haru (Babba )ya haye kan karagar mulki a matsayin Sarkin Hadejia ya yi shekara 20 yana mulki inda ya kawo sauye- sauye a masarautar Hadejia,ya kara bunkasa Ganuwar zuwa yadda take a halin yanzu.Ya gabatar da mulkinsa inda ya kara daukaka tafarkin addinin musulunci ta hanyar bude makarantun Islamiyya da kuma kiran Malamai wadanda suka san al’amarin musulunci daga sauran masarautu. Bai tsaya a nan ba domin kuwa an samu labarin cewar yana  masana addinin musulunci akan hanyarsu ta zuwa Makka inda yake basu shawarar su zauna a Hadejia saboda sha’awar da yake da ita ta yada addinin musulunci.

Bugu da kari lokacin shi ne aka kara fadadad Masallacin Jumma’ar birnin Hadejia inda  ya kara kasancewa babba.Ta bangaren zamantakewa da bunkasa tattalin arzikin ya tsarin ya ya jawo hankalin ‘yankasuwar kasshen  waje zuwa kasuwannin Hadejia. Ya yi hakan ne ta rage harajin shigowa da wasu kaya.Bayan nan kuma ya yaki wadanda ba musulmi ba wasu wuraren  Kare-Kare da Bade,wannan shi ya yi sanadiyar hada Adiani zuwa masarautar  Hadejia.Hakanan ma  a zamanin  sarautar Haru ne aka kawo karshen yawan zaman Manja da Doya da ake yi tsakanin Hadejia da Gumel  inda aka yi babban yaki a Zaburam  shekarar 1872, a lokacin ne aka kashe Sarkin Gumel  Abdu Jatau. Wannan nasarar ce ta kawo karshen yawan yake- yaken da ake yi tsakanin Hadejia da Gumel. Sakin Hadejia Haru ya mutu a shekarar 1885.(Taskar Suleiman Ginsau)